Zelensky na son ganawa da Putin don kawo ƙarshen yaƙi

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensk, ya wallafa wata buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga takwara aikinsa na Rasha, Vladimir Putin, inda ya gayyace shi zuwa ganawar ido-da-ido domin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi.
Wasiƙar, wadda aka wallafa a shafin intanet na shugaban Ukraine, ta ce a daidai lokacin da hankalin Amurka ya karkata gaba ɗaya kan rikicin Iran, ba zai dace a ci gaba da jiran lokacin da yaƙin Turai zai sake zama babban abin da Amurka za ta mayar da hankali a kai ba.
Zelensky ya kuma ce ƴan Rasha sun fara gajiya da hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da Ukraine ke kaiwa, da kuma matsalar hauhawar farashin kaya da ƙarancin man fetur, don haka a shirye suke su ga an samar da zaman lafiya.
Sa'o'i kaɗan bayan fitar da wasikar, fadar mulkin Kremlin ta Rasha, ta yi martani da cewa ana maraba da Mista Zelensky a birnin Moscow, idan har da gaske yana son ganawa ne da shugaba Putin.












